✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kashe N3.9bn don biya wa ɗaliban Kano kuɗin jarrabawar NECO da NBAIS

An ƙara yawan ɗaliban da gwamnatin ke biya wa daga kaso 34 zuwa kaso 83 a jarrabawar NECO.

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta ware Naira biliyan biyu da miliyan ɗari tara don biya wa ɗaliban jihar kuɗin jarrabawar NECO da ta NBAIS.

Wannan mataki wani yunƙuri ne na rage wa iyayen yara nauyin biyan kuɗin jarrabawar wanda galibi ke zama dalilin da yara ke daina zuwa makaranta.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dokta Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudana a Kano.

Doguwa ya bayyana cewa, duba da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ga dacewar a ƙara yawan ɗaliban da gwamnatin ke biya wa daga kaso 34 zuwa kaso 83 a jarrabawar NECO da kuma kaso 52 zuwa kaso 9 a jarrabawar NBAIS.

Kwamishinan ya bayyana cewa, a yanzu duk ɗalibin da ya samu kiredit huɗu a kowane darasi a jarrabawar gwaji wacce ke zama a matsayin ma’auni na hazaƙar ɗalibin don rubuta jarrabarwarsu NECO (Qualifying Exams) zai amfana da wannan shirin.

“A baya gwamnatin tana biya wa ɗalibin da ya sami kiredit takwas ko shida a jarrabawar gwajin ne kawai sannan kuma dole sai ɗalibi ya ci darussan Turanci da Lissafi. Hakan ya sa a yanzu fiye da ɗalibai 144,650 ne za su amfana,” in ji shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa ko a baya sai da gwamnatin ta biya  bashin da ta gada daga gwamnatin da ta gabata na ɗaliban juhar da suka rubuta jarrabawar NBAIS  kafin daga bisani aka ba su sakamakon jarrabawar ta su.

“Bayan da muka karɓi gwamnati mun tarar da ɗimbin bashi da ake bin gwamnati na jarrabawar NBAIS na shekarar 2021 da 2022 da 2023, wanda ya janyo ɗalibai ba su sami sakamakon jarrabawarsu akan lokaci ba.”

Doguwa ya yi kira ga iyayen yara da su yi ƙokari su tabbatar ‘ya’yansu suna zuwa makaranta bayan rubuta jarrabawar tantancewa, inda ya sha alwashin ɗaukar mataki akan duk ɗalibin da aka samu ba ya zuwa makaranta.

“Don yaro ya yi jarrabawar tantancewa ba hujja ba ce ya daina zuwa makaranta.

“Dole yaro ya ci gaba da zuwa makaranta har sai ya gama rubuta jarrabawar NECO.

“Za mu je makarantu mu duba duk ɗalibin da muka samu ba ya zuwa makaranta zai fuskanci hukunci, saboda ba ma son a samu nakasa karatun yaranmu.”

Haka kuma, Kwamishinan ya ja kunnen shugabannin makarantu da jami’an da ke kula da jarrabawa da su daina ɗabi’ar nan ta canza sunan ɗalibai ko maye gurbinsu da sunan wasu  a lokacin jarrabawa.

“Muna kira ga shugabannin makarantu da masu kula da jarrabawa kan maye sunan ɗaliban da ke makarantar da wasu.

“Duk wanda muka kama da wannan laifin ba zai ji daɗi ba, domin zai fuskanci hukunci mai tsanani.”