Gidajen burodi sun ce ‘yan Najeriya su kwana da shirin samun karin kashi 50 a farashin burodi sakamakon hauhawar farashin kayan hada burodin.
Kungiyar Masu Gidajen Burodi ta Najeriya (AMBCN) ta ce ba ta da zabi face yin karin domin ta nemi masu kayan hadin burodi su yi musu sauki, amma suka ce su ma ba su da zabi, saboda tsadar Dala.
- Babu dalilin kara kudin fetur ko lantarki —Kwankwaso
- Yadda za a dandake mata masu fyade a Kaduna
- Yadda ‘yan kasar waje ke juya farashin fulawa a Najeriya
Shugaban kungiyar, Raji Omotumbo, ya sanar a ranar Juma’a cewa, “Farashin dukkanin kayan hada burodi sun yi mummunar tashi musamman fulawa da sukari.
“Daga watan Maris zuwa Satumba, duk wata sai an kara N500 a farashin buhun fulawa, kuma masu gidajen burodi ke dauka.
“Babu riba a gasa burodi ko sayar da shi a farashinsa na yanzu.
“Mun yi ta rokon masu fulawa amma suna gunaguni game da wahalar samun Dala da kuma tsadarta.
“Yanzu zabin da ya rage mana shi ne mu roki gwamnati ta kawo mana dauki”, inji shi.