Majalisar zartarwa ta Jihar Nasarawa ta amince da kafa ma’aikatar raya karkara a jihar.
Ana sa ran dai sabuwar ma’aikatar za ta rika gudanar da dukkannin ayyukan raya kasa a yankunan karkara da suka hada da samar da hanyoyi, wutar lantarki da kuma ruwan sha.
Kwamishinan Yada Labarai, Al’adu da Yawon Bude Ido na jihar, Dogo Shammah shine ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai karin bayani jim kadan da kammala taronsu majalisar na wata-wata.
Ya ce hukumar za kuma ta kula aikin ginawa da kula da kananan hanyoyi tare da inganta su hadi aikin samar da ruwan sha a duk fadin jihar.
Kazalika, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta amince cewa daga yanzu tilas bangarori, ma’aikatu da hukumominta su rika tattara bayanai ta hanyar sabuwar fasahar sadarwa domin tafiya da zamani.
Kwamishinan ya ce hakan na cikin kudurin da gwamna Abdullahi Sule yake da shi na ganin cewa jihar ta shiga sahun jihohi uku a Najeriya da baki masu zuba ke sha’awar zuwa a Najeriya.