Gwamnan jihar Kano, Abdullahin Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta kafa cibiya ta musamman domin kula da masu larurar mata-maza a jihar.
Ya ce za a kafa cibiyar ne da hadin gwiwar Cibiyar Binciken TEFFund dake Jami’ar Usman Danfodiyo a Sakkwato.
- ’Yan bindiga sun kai hari Asibiti a Kaduna, sun sace ma’aikata
- Ya auri kanwarsa da ta bace tun tana jaririya
Ganduje, a cewar wata sanarwa da Kakakinsa, Abba Anwar ya fitar ranar Alhamis, ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar mutum bakwai da gwamnatinsa ta dauki nauyin yi wa aiki daga cibiyar jami’ar ta Danfodiyo kuma suka warke yayin wani kwarya-kwaryar biki a Gidan Gwamnatin jihar ranar Laraba.
Gwamnan ya ce, “Yanzu haka mun kudiri aniyar gina makamanciyar wannan cibiya a Kano tare da hadin gwiwar wannan cibiyar ta Jami’ar Danfodiyo, da nufin tallafawa masu fama da wannan larurar.
“Jihar Kano ta damu matuka lokacin da muka sami rahoton akwai wani mutum daya dake fama da wannan larurar kuma yana bukatar a yi masa aiki.
“Nan da nan muka ba da umarnin a kai shi wannan cibiya kuma a binciko mana sauran masu wannan larurar.
“Cikin ikon Allah mun sami karin mutum shida kuma Alhamdulillahi dukkansu mun yi musu aiki ga shi har sun warke,” inji Ganduje.
Ya kuma ce jihar ta bayar da umarnin a sake binciko karin masu wannan cutar, inda ya ce su ma jihar za ta dauki nauyin kula da su, kamar yadda wadannan mutum bakwai din suma ba su biya ko sisin kwabo ba.
Bugu da kari, Ganduje ya ce akwai yuwuwar duk wurin da ya fi yawan mutane a fi samun mutanen dake dauke da wannan larurar, inda ya ce kasancewar Kano jihar da ta fi kowacce yawan jama’a ba abin mamaki ba ne in ta sami yawan masu dauke da cutar.