Shugaban Majalisar Wakilai, Dokta Abbas Tajudeen ya ce Kasafin Kuɗin Nijeriya na baɗi zai ba da damar kafa ƙarin makarantu na matakin tarayya a mazaɓarsa ta Zariya.
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne lokacin babban taron shekara-shekara karo na 31 da 32 na ƙungiyar bunkasa ilimi ta Zariya, watau ZEDA da aka gudanar a Zariya.
- Mai Pataskum ya buɗe masallacin garin Danga a Yobe
- An kama mutum biyu kan kisan wata mata saboda maita
Ya bayyana cewa makarantun da ake shirin kafa wa sun haɗa da makarantar firamare da sakandare na yara masu buƙata ta musamman da kwalejin tarayya na koyon aikin noma da kiwo.
Shugaban majalisar ya kuma bayyana fara bada tallafin na musamman ga ɗaliɓin da ya fi kowa kwazo a fannin koyon ilimin kwamfuta da kuma ɗalibin da ya fi kowa nuna hazaƙa a bangaren makarantun sakandare da ke larɗin Zazzau.
Ya bayyana rashin jin daɗi bisa jinkirin da aka samu wajen biyan ɗalibai 2500 kuɗin tallafin karatu da suke lardin Zazzau, yana mai cewa za a ƙara yawan ɗaliban da za su riƙa cin moriya tallafin zuwa 3000 a shekarar 2026.
Shugaban majalisar ya ɗora alhakin jinkirin da aka samu wajen biyan tallafin akan kaddamar da kasafin kuɗin shekarar 2024, inda ya bayyana cewa za a biya kuɗin da zarar al’amura sun daidaita.
Haka kuma, ya ba da sanarwar cewa zai gina wa ƙungiyar ZEDA tare da sanya kayayyaki irin na zamani a ɗakin taro da zai ɗauki kimanin mutane dubu ɗaya.
Shugaban majalisar ya ƙara da cewa kudurin majalisar ne ganin ta bunkasa ilimi a matakin farko da inganta ilimin sakandare da na kimiyya da kawo sauyi a fannonin ƙirƙira.
Ya buƙaci kungiyar ZEDA da ta ɓullo da wani tsari da zai samar da yanayin bai wa malamai horo da shigar da iyaye cikin harkokin tattauna batutuwan da suka shafi ilimi.
Tun farko a jawabinsa na maraba, shugaban kwamitin tsare-tsare na kungiyar ta ZEDA, Dokta Abdul Alimi Bello ya ce kungiyar ta sami gagarumar nasara da ya nuna aniyar ta na samar da ingantaccen ilimi da bunƙasa al’umma.
Ya ce cikin shekaru da dama, ƙungiyar ta kasance jagoran kungiyoyi masu zaman kansu a lardin Zazzau da suke kula da ilimin zamani da bunkasa sana’o’in hannu.
A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya buƙaci ƙungiyar da ta yi amfani da kuɗaɗen shigar ta wajen tabbatar da samar da kyakkyawan sauyi a ɓangaren ilimi.