Gwamnatin Tarayya ta ce ta kammla shirye-shiryen kaddamar da aikin kananan ma’aikata 774,000 da za su yi mata aikin wucin gadi.
Sau uku gwamnati na dage kaddamar da shirin na SPW, kafin daga baya Minista a Ma’aikatar Kwadago, Festus Keyamo ya ce za a fara a watan Janairun 2021.
- ’Yan ta’adda sun yi wa mafarauci yankan rago a Abuja
- ‘Na yi nadamar mai da kaina namiji’
- Zamfara: An cafke mahara a Fadar Sarkin Shinkafi
- MURIC ta bukaci a nemi mafitar magance Boko Haram
Keyamo ta shafinsa na Twitter, ya ce, “Shugaban Buhari ya ba da izinin kaddamar da SPW (na kananan ma’aikatan wucin gadi 774,000) a fadin Najeriya ranar Talata, 5 ga Janairu, 2021.
“Ofisoshin Hukumar Samar da Ayyuka ta Kasa (NDE) a dukkannin jihohi sun shirya tsaf domin bikin kaddamar da shirin”, inji shi.
Gwamnati ta bullo da shirin SPW da zai dauki kananan ma’aikatan wucin gadi 1,000 daga kowacce daga cikin Kananan Hukumomin Najeriya 774.
An ware wa shirin wanda da farko aka tsara kaddamarwa ranar 1 ga Oktoban 2020, biliyan N46.44 daga cikin biliyan N60 na kudin tallafin COVID-19.
Ministar Kudi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce a wata ukun da za su yi aikin, za a rika biyan ma’aikatan albashin N20,000 a kowane wata.
A baya can, Gwamanatin Tarayya ta dakatar da shirin bayan sa-toka-sa-katsi tsakanin Keyamo da Darakta-Janar na NDE, Nasir Ladan, wanda aka sallama a ranar 8 ga watan Disamba, 2020 kan jagorancin shirin.