✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a je zagaye na biyu a zaben Shugaban Faransa

Za a sake fafatawa ne tsakanin Emmanuel Macron da Marine Le Pen

Biyo bayan gaza samun wanda ya yi nasara zagayen farko na zaben Shugaban Kasar Faransa, a yanzu dai ta tabbata Emmanuel Macron zai sake fafatawa da babbar abokiyar hamayyarsa, Marine Le Pen a zagaye na biyu.

Za a gudanar da zaben ne ranar 24 ga watan Afrilun 24, tsakanin Shugaba mai ci da Misis Marine, mai ra’ayin rikau, bayan gaza samun wanda ya yi nasara a zagayen farko na ranar Lahadi.

Shugaba Macron dai ya samu kaso 28.1 cikin 100 na kuri’in, yayin da ita kuma Marine ta samu kaso 23.1, sai mai biye musu baya, Jean-Luc Mélenchon, wanda ya samu kaso 22.

Tun bayan ayyana sakamakon zaben zagaye na farkon dai, sauran ’yan takarar tuni suka mika wuya.

Dukkansu dai, in ban da Eric Zemmour, sun bukaci magoya bayansu su zabi Macron, don hana Marine mai ra’ayin rikau darewa kujerar.

Yayin yakin neman zabe dai, Macron ya fi mayar da hankali a kan manufofin Faransa a kasashen waje, musamman yakin Rasha da Ukraine, ita kuwa Marine ta fi mayar da hankali ne a kan harkokin cikin gidan kasar, musamman tsadar kayayyaki, wacce masu zabe suka ce ita ce babbar matsalarsu.

Zaben dai ya maimaita kwatankwacin irin wanda aka fafata tsakanin ’yan takarar biyu a zaben 24 ga watan Afrilun 2017, wanda Macron ya lashe da gagarumin rinjaye.

Akalla masu zabe miliyan 48.7 ne suka yi rajistar zaben a fadin kasar.

%d bloggers like this: