Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce za a iya kawo karshen ’yan bindiga a wata 16 da suka rage wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Gwamnan na wadannan kalaman ne a wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise ranar Asabar, inda ya ce wurin da ’yan bindigar suke ba boyayye ba ne.
- An kona motoci 874 a Faransa saboda murnar sabuwar shekara
- Yadda za a magance fitowar gemu a fuskar mace
A cewar Gwamnan, jami’an tsaron sun san abin da za su yi su magance matsalar tsaron.
Ya ce muddin aka gaza kawo karshen matsalar a cikin lokacin, to tabbas akwai masu amfana da ita.
“Za mu iya gamawa da wadannan mutanen idan muka jingine batun hakkin bil Adama a gefe da zai iya zuwa daga kasashen waje. Ai su ba fatalwoyi ba ne.
“Mun san inda suke, za mu iya gamawa da su. Ba lallai ne gwamnati mai ci ta iya kammala aikin ba, amma za ta iya cin karfin matsalar.
“Sai dai idan akwai masu amfana da matsalar daga cikin jami’an tsaro, amma babu makawa za a iya murkushe su,” inji Fayemi.