✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a hukunta wadanda suka saka bayanan jima’i a littafin ‘yan firamaren China

Ma’aikatar Ilimin kasar China, ta ce mutum 27 ne suka fuskanci fushinta saboda binciken da ta yi kan wani zanen tsiraici da aka yi a…

Ma’aikatar Ilimin kasar China, ta ce mutum 27 ne suka fuskanci fushinta saboda binciken da ta yi kan wani zanen tsiraici da aka yi a littafin karatun daliban Firamaren kasar.

Ma’aikatar ta ce ta yi hakan ne domin samunsu da laifin rashin yin aiki yadda ya kamata, wanda ka iya janyo mummunan rashin fahimta, bayan labarin ya karade kafofin sada zumunta a kasar.

Kazalika, ma’aikatar ta kuma ce ba za a sake amfani da ayyukan Wu Yong, mai zanen bangon littafin Lyu Min da Lyu Jingren da ma duk tarurrukan bitarsu ba, wajen tsara litattafan kasar baki daya.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce salon zanen ya saba wa abin da al’ummar kasar ke so, don haka ta soke amfani da shi a makarantun.

Hukumar Wallafa littattafan Dalibai ta Kasar (PEP), ta ce ta kammala shirin sake fasalin littafan lissafi ga daliban firamare.

Haka kuma, ta ce tana iya bakin kokarinta don ganin ta sabunta littattafan kafin shiga sabon zangon karatu a watan Satumba.

Dambarwa kan littattafan ta fara ne bayan da wata mata ta dauki hoton wasu shafuka daga ciki ta watsa a kafafen sada zumunta, wadan ke dauke da hotuna da bayanai kan jima’i, auren jinsi, da wariyar launin fata

Duk da wasu sun yaba da littafin cewa zai taimaka wa daliban samun ingantaccen ilimin fannin ba gurbatacce ba, da kuma ba su ilimi kan auren jinsi da sauran mas’a’loli da suka fara karbuwa a kasashen duniya da dama.

Sai dai da dama na ganin hakan bai dace ba, kasancewar kananan yaran da shekarunsu ba su kai na balaga ba ne ke daukar wannan karatun.