Wani malami a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) Mohammed Shu’aibu Atabo, ya koka kan yajin aikin kungiyar malaman jami’ai (ASUU) da ya ki ci ya ki cinyewa.
Malamin ya ce yanzu haka shekara guda ke nan da ya ki karbar aikin koyarwa a Dubai, gabanin fara yajin aikin a watan Fabrairu don kishin Najeriya.
- ISWAP ta hallaka mayakan Boko Haram da ke tsere wa sojoji
- Lauyoyin Kano sun maka Ado Gwanja da Safara’u a kotu kan lalata tarbiyya
Ta wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Muhammad ya ce a ranar Laraba ya cika shekara guda da kin karbar aikin.
“Ni na nemi aikin, kuma cikin mutane 200 da suka nema a fadin duniya, ina sahun gaba na wadanda aka bai wa.
“Sai dai daga baya na canja shawara, sakamkaon ganin kasata na da bukata, kuma bai kamata na tsallake ta ba.
“Ba surutun da ba a yi min ba, har a gidanmu, amma na toshe kunnena.
“Yanzu ba abin da nake banda nadama, saboda Gwamnatin Najeriya ba ta san martabarmu ba.
“Shi ya sa matasa da sun samu aiki ko yaya yake a waje, suke tsallake kasar.”
Ya ce tsawon lokacin da ASUU ta shafe tana yajin aikin, madadin gamnati ta kawo karshensa, sai ta tsaya yi musu barazana da kin biyan su albashi.
Yanzu sama da wata shida ke nan da malaman ke yajin aiki, sakamakon gazawar Gwamnatin Tarayya wajen biyan bukatunsu na farfado da jami’o’in gwamnati da biyansu kudaden alawus-alawus, hadi da amfani da tsarin (UTAS) wajen biyan su albashi.
Sai dai ana ta samun sa toka-sa-katsi kan tttaunawa tsakanin ASUUn da Gwamnati har ya zuwa yanzu.