Shugaban Kasa Muhammadu Buari ya yi ganawar sirri da Shugaban Majalisar tarayya Femi Gbajabiamila, kan yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU).
Shugaban Majalisar ya bayyana wa manema labarai cewa akwai alamun nasara a ganawar da suka yi ranar Talata a Abuja da Buharin.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Kishiyar ASUU Rajista
- NUT ta bukaci gwamnoni su biya malamai basussukan da suke bi
Ya kuma ce Shugaban Kasar ya yi alkawarin nazarin shawarwarin da Majalisar ta bayar kan yadda za a warware turka-turkar da ke tsakanin gwamnatin da ASUU.
“Shugaban kasa ya amince da shawarwarin da muka dau tsawon lokaci muna ganawa da shi kansu, kuma ya ce zai je ya nazarce su.
“Ranar Alhamis za mu sake dawowa mu yi zaman karshe kan batun idan Allah Ya kai mu”, in ji Gbajabiamila.
Ya kuma bayyana cewa shawarwarin da suka mika wa shugaban sun tattaro su ne a tarurruka daban-daban da suka gudanar da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.
Kazalika ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa nan ba da dadewa ba za a kawo karshen yajin aikin, domin bangarorin biyu (ASUU da Gwamnatin Tarayya) sun amince da sanya kasar a gaba madadin son zuciyoyinusu.