Ministan Yada Labarai da Al’adu Lai Mohammed, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya inganta Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015.
Ya kuma ce fiye da shekaru 30, ‘yan Najeriya ba su san yin tafiye-tafiye ta jirgin kasa ba sai da Buhari ya dawo karagar mulki.
- Masu zanga-zanga kan canjin kudi sun kona bankuna 2 a Ogun
- Saudiyya ta tsare ‘yan Najeriya 800 —NiDCOM
Ministan ya bayyana hakan ne a ta wani shiri na gidan talabajin na NTA ranar Litinin, inda ya ce duk da kokarin dakile gwamnatin da wasu tsiraru ke yi sai da ta kammala hanyar jirgin kasan Legas zuwa Ibadan, da Abuja zuwa Kaduna, da Ajakuta zuwa Warri, wadanda a baya babu su.
Ya ce, “Mun raya kasar nan fiye da yadda muka same ta a 2015 da PDP ta kammala mulkinta.
“Haka kuma Buhari ya cika alkawura da bukatun ‘yan Najeriya, a wa‘adin da ya ce musu zai yi.
“Yunkurin da wasu kalilan ke yi na bakanta gwamnatin a idon talakawa ba zai yi nasara ba.
Ya ce a bangaren tsaro ma ‘yan Najeriya ba sa bin Buhari bashi, domin lokacin da yau mulki baki daya yankin Arewa maso Gabas ba ya shiguwa, kuma kananan hukumomin Jihar Borno 20 na karkashin ikon ‘yan Boko Haram ne.
“Amma yanzu babu wani yanki na kasar nan da ke karkashin ikon ‘yan ta’adda,” in ji Ministan.
Lai ya kuma ce a bangaren abinci kuwa, a shekarar 2015 Najeriya ce ta daya a kasashen da ke shigo da shinkafa daga kasar Thailand, amma yanzu sabbin tsare-tsaren noma da gwamnati ta kirkiro sun sa ta wadatu da abinci.
“Shirin Anchor Borrowers da miliyoyin manoma suka amfana da shi ya samar musu da hanyoyin dogaro da kai, baya ga masarrafar shinkafa da ta karu daga biyu tak da muke da su a 2015 zuwa 60 a 2023″ in ji shi
Ya kuma ce Buhari ya yi hanyoyi da suka kai jimillar nisan kilomita 17,000, da kuma gyara masu nisan kilomita 8,000.