✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu da masaniyar masu neman kai Tinubu kasa —Gwamnati

Gwamnati ba ta san da wasu ma su yi wa Tinubu zagon-kasa ba

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da masaniyar cewa akwai makiya a Fadar Shugaban Kasa da ke kokarin kayar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a zabe mai zuwa.

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed ne ya fadi hakan a matsayin martani ga zargin da Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi.

“Idan akwai mai yi wa wani dan takara zagon kasa, ba mu san da hakan ba a hukumance,” in ji Lai.

El-Rufa’i dai ya yi zargin cewa akwai makiyan Bola Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da suke kokarin ganin sun kai shi kasa a zaben da ke tafe.

Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na Sunrise Daily da safiyar Laraba.

Sai dai ministan ya ce a hukumance gwamnati ba ta san ko mutum guda da ke da wannan kudiri ba a Fadar Shugaban Kasa.

Ya ce gwamnati ta kasance mai adalci ga kowa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba kuma a koyaushe Shugaba Buhari kan nuna shi mai son ganin an yi sahihin zabe ne mai cike da adalci.

“Sahihin zabe kuwa ba yana nufin fifita wani ko cin mutuncin wani ne ba, kuma duk inda ya je yakan bayyana hakan,” in ji ministan.

A hirar da aka yi da El-Rufa’i ya ce, “Na tabbata a Fadar Shugaban Kasa akwai masu son mu fadi zaben nan, saboda bukatarsu ba ta biya ba, an kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani.”