Babban Daraktan Muryar Najeriya (VON), Mista Osita Okechukwu, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya wargaza aniyyar tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ta neman wa’adi na uku a 2003
Okechukwu wanda guda ne daga jiga-jigan da suka kafa jam’iyyar APC, ya ce batun da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, kuma dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi na cewa shi ne ya wargaza aniyyar Obasanjon ba gaskiya ba ne.
“Gaskiya ne da aka zo karshen lamarin Atiku ya shiga ciki, amma batun shi ne ya dakatar baki daya ba gaskiya ba ne.
“Da yawa daga cikinmu sun san yadda Obasanjo ya yi kokarin maida Najeriya turbar siyasar jam’iyya daya, da kuma kokarin yin zango na uku a matsayin shugaban kasa.
“Buhari ne ya watsa shirin ta hanyar karfafa jam’iyyar adawa ta lokacin wato APP, har ya samu kuri’a miliyan 12 a zaben shugaban kasa na 2003.
“Don haka shi ne za a ce ya wargaza wancan shirin, ya kuma yi fatali da tsarin siyasar jam’iyya daya, da batun yin zango na uku na shugabancin kasa” in ji Okechukwu.