Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yanzu haka ’yan adawar siyasa a ƙasar nan a shirye suke su ƙalubalanci shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Tun bayan da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku ya riƙa yin taro da ’yan adawa don neman karɓe mulki daga hannun jam’iyya mai ci.
- Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe
- Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati
Da yake jawabi ga manema labarai tare da wasu ’yan adawa a zauren taro na ‘Yar’adua Center da ke Abuja a ranar Alhamis, Atiku ya ce an yi taron ne don sake samar da wasu ‘yan adawa kafin babban zaɓe mai zuwa.
Da yake amsa tambayoyi kan ko taron manema labarai na ƙawancen ‘yan adawa na nuni da haɗuwar jiga-jigan ‘yan adawa? Atiku ya ce, “Wannan ita ce samar da haɗakar ‘yan adawa gabanin 2027”.
A ranar Talata ne shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, inda ya kori gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da ’yan majalisar dokokin jihar, lamarin da ya sa ’yan adawa suka mayar da martani.
Da yake jawabi ga manema labarai a madadin shugabannin adawa a a zauren taron a Abuja, ranar Alhamis Atiku ya zargi Tinubu da son zuciya.
Sauran jiga-jigan ’yan adawa da suka halarci taron manema labarai sun haɗa da: Tsohon Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, wanda Yunusa Tanko ya wakilta, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sakataren haɗakar jam’iyyun siyasa na ƙasa, Peter Ameh, da dai sauransu.