Hukumar gudanarwar Jami’ar Benin ta musanta labarin da ake yadawa cewa za ta koma bakin aiki a ranar 20-ga oktoban 2022.
Jita-jitar dai ta fara yawo ne mako biyu bayan jami’ar ta saki sakamkaon daliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’ar ta Oost UTME da Direct Entry.
- Sarkin Kano ya koka kan dabi’ar rashin karantun littafai a tsakanin matasa
- HOTUNA: Bikin Maulidi a wasu kasashen duniya
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun kakakinta, Benedicta Ehanire, jami’ar ta shawarci daliban da ma iyaye da sauran al’umma, da su yi watsi da jita-jitar.
Haka kuma ta ce har zuwa yanzu jami’ar ba ta sanya ranar komawa aiki ba.