✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku nemi tallafin mawadata da kungiyoyi —Gwamnati ga jami’o’i

Adamu Adamu ya ce sharadin nada shugaban jami'a daga yankin da ya fito ya lalata ingancin ilimi a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta shawarci shugabannin jami’o’in Najeriya da su nemi tallafi n masu kudi da kungiyoyi domin samun karin kudaden shiga.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya yi kiran ne a yayin da yake kaddamar da majalisar gudanarwar Jami’ar Aikin Gona ta Abeokuta, da ta Micheal Okpara da ke Umdike, da ta Joseph Saruwuan Tarka da ke Makurdi, da kuma ta Zuru.

Adamu Adamu, wanda Minista a Ma’aikatar Ilimi, Goodluck Opiah ya wakilta a ranar Alhamis, ya ce matsin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki, ya sanya gwamnati neman janyo kamfanoni masu zaman kansu cikin harkar ilimi a manyan makarantu don samun karin kudaden shiga.

“Muna kira gare ku, da ku lalubo wasu hanyoyin samun karin kudaden shiga, musamman daga daidaikun mutane masu taimako, zuwa kungiyoyi, don karawa a kan na gwamnati, don tsayawa da kafarku.

“Idan kuka yi haka, za ku fi samun girmamawar al’umma da kuma ciyar da ilimin gaba,” in ji shi.

Ministan ya kuma ce sharadin sanya shugaban jami’a ya zama ya fito daga yankin da take, ya lalata ingancin ilimin Najeriya ainun.

Adamu Adamu ya ce kamata ya yi a ce cancanta ake fifitawa ba yankin da mutum ya fito ba.