Gwamnatin Tarayya ta bayyana hasashen cewa Najeriya za ta samu kudin shiga da ya kai Dala miliyan 500 ta hanyar fitar da kwallon kashu zuwa ketare a bana.
Ministan Harkokin Noma da Raya Karkara, Dokta Mohammed Abubakar wanda ya yi wannan furuci, ya kudin shigar da za a samu ya saba wa Dala miliyan 250 da aka samu bara.
- Har yanzu ban taba ganin sabbin takardun Naira ba —Gwamna Ortom
- Na tafka kuskure a tafiyar Buhari, ba zan maimaita da Tinubu ba — Naja’atu
Abubakar ya bayyana haka ne ta bakin Sakataren Ma’aikatarsa, Dokta Ernest Umakhihe a wajen taron Ranar Kashu ta Kasa da aka shirya ranar Talata a Abuja.
Ya ce, “A Najeriya, amfanin kashu na dada karuwa duba da yadda a kan fitar da shi kasashen ketare tun a shekarun 1990.”
Ya kara da cewa, kashu ya zama hanyar samun kudin shiga ga kasa wanda ba man fetur ba.
“An yi kiyasi cewa shi ne ya samar da sama da kashi 10 cikin 100 na tattalin arzikin da aka samu ta hanyar fitar da kaya ketare a 2022,” in ji shi.
Kazalika, Ministan ya ce kashu ya zama daya daga cikin amfanin gona masu kawo kudi, kuma ana noma shi a jihohin kasar nan 27 ciki har da Abuja.