✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a hau jirgin kasa kyauta tsawon mako 1 albarkacin Kirsimati – Gwamnati

Gwamnati ta ce ta fito da garabasar ne don saukaka wa jama'a wahalhalun tafiya.

Gwamnatin Tarayya a ranar Juma’a ta sanar da cewa za a hau jirgin kasa kyauta a duk fadin Najeriya na tsawon mako daya albarkacin bukukuwan Kirsimati da na sabuwar shekara.

Za a fara cin gajiyar tagomashin ne daga ranar Juma’a, 24 ga watan Disamban 2021 zuwa ranar hudu ga watan Janairun 2022, kamar yadda Kakakin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Mahmoud Yakubu ya tabbatar a cikin wata sanarwa.

Ya ce garabasar za ta shafi dukkan sassan jiragen kasar da hukumar ke gudanar da su.

Hanyoyin da garabasar za ta shafa sun hada da Abuja zuwa Kaduna da Legas zuwa Ibadan da Warri zuwa Itakpe da Kano zuwa Legas da Minna zuwa Kaduna da kuma Aba zuwa Fatakwal.

Shi ma Shugaban hukumar ta NRC, Injiniya Fidet Okhiria, ya ce, “Mun yanke shawarar yin garabasar ne da hadin gwiwar Ma’aikatar Sufuri don saukaka wa jama’a wahalhalun da suke fuskanta yayin tafiye-tafiye lokacin bukukuwan Kirsimati.

“Hakan zai taimaka musu wajen rage yawan kashe-kashen kudade kuma su yi zirga-zirga cikin sauki.

“Sai dai muna ba fasinjoji shawarar su yi kokarin samun tikitinsu daga wuraren da aka tanada a kyauta, domin su sami damar shiga jiragen.

“Kazalika, fasinjojin za su kiyaye da dokokin cutar COVID-19 na sanya takunkumi da kuma wanke hannuwa a kai a kai.” inji shi.

Ya kuma ce gwamnati za ta tabbatar da tsaro da kare lafiyar fasinjojin yayin wannan lokacin.