An gudanar da addu’o’i na musamman ga Fira Ministan Najeriya na Farko, Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa, yayin bikin Ranar Tunawa da ’Yan Mazan Jiya na Najeriya na 2021 a Jihar Bauchi.
A yayin lakcar tunawa da marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa da aka gudanar a addu’o’in ne Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar cewa ta kammala shirye-shirye gyara kabari da kuma gidansa.
- Bom ya kashe sojoji 5, ya jikkata 15 a Borno
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
- Iyaye sun yi karar saurayin ’yarsu kan fasa auren ta
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 14 a Jihar Kogi
Kwaminshinar Raya Al’adu da Harkokin Yawon Bude Ido, Asma’u Ahmed Giade, ta ce Gwamnatin Jihar ta dauki gabarar aikin ne lura da cewa a tsawaon lokaci gwamnatocin da suka gabata sun yi watsi da gidan da makwancin marigayin yake.
Ta ce tuni gwamnati mai ci ta fara aikin yi wa wurin kwaskwarima ta yadda zai jawo hankalin masu ziyarar bude ido daga ciki da wajen Najeriya.
Kwamishinar ta ce, a shekarar 2020 ce Gwamna Bala Mohammed ya ayyana ranar 15 ga watan Janairun kowace shekara a matsayin ranar yin addu’o’i na Musamman ga marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa, kuma Majalisar Dokokin Jihar ta yi dokar da ta tabbatar da hakan.
Najeriya ta ware ranar 15 ga Janairun duk shekara a matsayin ranar tunawa da ’yan mazan jiya da suka sadaukar da rayuwarsu domin tabbatar da dorewar kasar a matsayin dunkulliya —cikinsu har da sojojin da suka halarci yakin basasa da sauransu.
An zabi ranar ce kasancewar a makamanciyarta sojoji masu juyin mulki suka hambarar da zababbiyar gwamnatin Najeriya ta farko bayan samun ’yanci.
A jurin mulkin ne sojoin suka kashe marigayi Tafawa Balewa da Firimiyan Jihar Arewa na farko, Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da sauran manyan shugabanni a wancan lokaci.