Za a gudanar da gasar gwarzon dan kwallon Afirka da kamfanin sadarwa na GLO tare da hadin gwiwar Hukumar Shirya kwallo ta Afirka (CAF suke daukar nauyi a duk shekara a Legas.
Za a yi biki ne a ranar Alhamis 8 ga watan Janairun 2015 inda ake sa ran halartar shahararrun ’yan kwallo da masu horar da suka fito daga sassa daban-daban a Afirka don a ba su kyaututtuka daban-daban.
Daga cikin kyaututtukan da za a raba akwai na Gwarzon dan kwallon Afirka da kuma wasu guda 15 da suke biye da shi.
Sauran kyaututtukan su ne na Gwarzon dan kwallon Afirka (na ’yan kwallon da ke wasa a Afirka) da kungiyar kwallon kafa ta kasa da ta fi fice, da kulob din da ya fi samun nasara da mai horarwar da ya fi samun nasara.
Sauran sun hada da matashin dan kwallon da ya fi nuna kwazo, da kungiyar kwallon kafa ta mata da ta fi samun nasara da Gwarzuwar ’yar kwallon kafa ta mata a Afirka da srauransu.
Haka kuma a ranar ce za a zabi gwarzayen ’yan kwallo goma 11 da za su kasance a matsayin kungiyar kwallon kafar Afirka ta shekarar 2014.
Yaya Toure, dan kwallon Kwaddebuwa da yanzu haka yake buga wa kulob din Manchester City na Ingila ne ya lashe kyautar har sau uku a jere. Ya lashe ta bara wanda aka yi bikinta a Legas a ranar 9 ga watan Janairun wannan shekarar da muke ciki.