✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fara rataye ’yan bindiga a Neja

Ya kuma ce masu samar musu da bayanai su ma yanzu rataye su za a rika yi.

Gwamnatin Jihar Neja ta amince da wasu sabbin dokoki da za su sa a fara rataye ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da barayin shanu da kuma masu samar musu bayanai a Jihar.

Hakan dai ya biyo bayan wasu dokoki da Gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello ya rattaba wa hannu.

A yayinn wani kwarya-kwaryar taro da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Minna ranar Juma’a, Gwamnan ya ce asalin Dokar Satar Mutane da ta Shanu ta 2016 ce aka yi wa kwaskwarima domin a hada da masu basu bayanai a cikin wadanda hukuncin zai shafa.

Ya kuma ce masu samar musu da bayanan wadanda sune kanwa uwar gami wajen taimaka wa aika-aikar, su ma yanzu za su fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya.

“Duk wanda ya tunzura wani mutum domin ya yi garkuwa da wani ko ya saci shanu, ko kuma da gangan ya tallafa wa kowanne irin yunkuri na garkuwa da mutane ko ta shanu, ya aikata laifin da zai iya fuskantar hukuncin kisa ta hanyar rataya,” inji Gwamna Sani Bello lokacin da yake karanto wani sashe na dokar.

Ya ce hukuncin wani muhimmin mataki ne da ya zama wajibi Jihar ta dauka domin magance kalubalen tsaron da ya addabi Jihar da ma kasa baki daya.