✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara karbar kudin ajiyar Maniyyata aikin Hajjin 2021

Za a ba da fifiko ga maniyyatan aikin Hajjin 2020 da suka bar kudinsu

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ya bayar da umarnin ci gaba da karbar kudin ajiya daga maniyyatan aikin Hajji na 2021 mai zuwa.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ya shaida wa manema labarai haka a ofishin hukumar.

Ya kara da cewa, Gwamnan ya ba da umarnin fara karbar kudin ajiyar na Naira dubu dari biyar wanda za a biya ta hanyar banki ga hukumar.

Ga wadanda suke da ajiyar kudin nasu da basu karba ba, za su ci gaba da biya har kafin a samu yawan adadin maniyyatan da Hukumar Aikin Hajji ta Kasar Saudiya ta kayyade tare da takwararta ta Najeriya (NAHCON).

Babban Daraktan ya kara jadda kudurin hukumar na fifita wadanda suka yi hakurin barin kudinsu na aikin Hajjin 2020 da Allah Bai sa aka samu yi ba.

“Komi wannan hukuma za ta yi ga maniyyatan to da su za a fara, wanda ya hada da tashinsu zuwa Kasa Mai Tsarki da zarar komai ya kammala.

“Sannan wadanda suka fara biya a yanzu za su zamo a sahu na biyu wajen kyautatawa.

“Saboda haka, kofa a bude take ga maniyyatan aikin Hajji na 2021,” inji Babban Daraktan hukumar alhazai ta Jihar Katsina.