Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce za a fara kame tare da hukunta iyayen da yaransu ba sa zuwa makaranta daga ranar 12 ga watan Satumba mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Benin, babban birnin jihar lokacin da yake yawabi kan matakan da aka dauka kan shirye-shiryen komawar sabon zangon karatu mai kamawa.
- China ta fuskanci zafi mafi tsanani tun 1961
- Tsofaffin Shugabannin Jami’o’i za su shiga tsakanin Gwamnati da ASUU
Gwamna Obaseki ya kuma ce tuni aka kafa kotuna na musamman domin hukunta wadanda ke cin zarafin mata a makarantun jihar.
“Idan muka kama kowanne yaro dan kasa da shekara 18 ana amfani da shi wajen aikatau, za a hukunta iyayensa. Muna godiya ga Babban Jojin jiharmu saboda samar da kotuna na musamman da za su hukunta irin masu cin zarafin yara a makarantunmu.
“Kazalika, daga ranar 12 ga watan Satumban 2022, lokacin da makarantu za su koma, duk yaran da aka kama suna gararamba ko talla a kan tituna lokacin makaranta, za mu kama iyayensa sannan mu dauki tsattsauran mataki a kan su.
“Mun horar da mutane da za su sa ido a kan cin zarafin yara a jihar Edo,” inji shi.
Gwamnan ya kuma ce ya umarci Ma’aikatar Ilimin jihar da ta rusa duk wani ginin da ya tsufa a cikin makarantu, tare da kai daliban wasu makarantun har zuwa lokacin da za a kammala gyare-gyaren.