✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shirin ‘Gidan Badamasi’ zango na 4 zai fito ranar 6 ga Janairu

Daraktan shirin ya ce shirin zai kayatar da masu kallo.

Za a fara haska shiri mai dogon zango da masu kallon fina-finan Kannywood ke jira, Gidan Badamasi zango na hudu a ranar 6 ga watan Janairu, 2022 a gidan talabijin na Arewa24.

Wanda ya shirya shirin ya kuma bayar da umarni, Falalu Dorayi, ya bayyana cewa zango na hudu na shirin ya zo da sabon salo da ya fi sauran na baya.

Dorayi, ya ce abin da ya bambanta zango na hudu da sauran na baya shi ne an dauke shi ne a sassa daban-daban na Jihar Kaduna.

Ya kara da cewa shi ne shiri na farko da ya fara karbar koken masu kallo tare da aiwatar da tsakurensu a cikin fim din.

“Gidan Badamasi zango na hudu zai kayatar da ’yan kallo saboda ya zo da bakon abu a cikin fina-finai masu dogon zango.

“Mun karbi tsakure daga masu kallo wanda shi ne ya sanya shirin [ya kasance] na musamman,” a cewarsa.

Shirin na dauke da manyan ’yan wasa da suka hada da Adam A. Zango, Mustapha Naburaska, Suleman Bosho, Dan Kwambo, Falalu A. Dorayi, Tijjani Asase, Umma Shehu, Hadiza Kabara, Ado Gwanja da sauransu.