✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za A Fara Daure Masu Jefar da ’Ya’yansu A Najeriya

Majalisar Dokoki ta Kasa ta kammala karatu na biyu kan kudirin dokar tura iyayen da suka jefar da ’ya ’yan da suka haifa zuwa gidan…

Majalisar Dokoki ta Kasa ta kammala karatu na biyu kan kudirin dokar tura iyayen da suka jefar da ’ya ’yan da suka haifa zuwa gidan yari.

Kudirin mai taken ‘Dokar Gyaran Guska Ga Dokar Kare Hakkin Kananan Yara ta 2004’, dan majalisa mai wakilatar Esan da ke Jiher Edo ne ya gabatar da shi.

Da yake gabatarwa a ranar Talata, dan majalisar ya ce, tanadin shi ne, “Ba za a yi watsi da wani yaro a lokacin da aka haife shi ko wurin da aka haife shi ba, komai kin jinin silar haihuwarsa.

“Kuma duk wanda aka samu ya saba wa wannan doka, zai biya tarar N200,000 ko ya fuskanci daurin watanni shida a gidan yari, ko ma a hada masa biyun duka.”

A cewarsa, kudirin na neman yin tanadi ne cikin dokar kare hakkin yara, game da yadda iyaye ke watsi da ’ya’yan da suka haifa, ta hanyar gabatar da sabon sashe na 3 a cikin sashe na 14 na Dokar.

Yanzu haka dai Majalisar ta mika kudirin ga kwamitin Harkokin Mata da Kananan Yara, domin ci gaba da nazarin sa ta fuskar shari’a.