Gwamnatin kasar Sri Lanka ta haramta wa ilahirin ma’aikatan lafiya da na lantarki da ke kasar shiga yajin aiki dungurungum.
Kazalika, an tanadi hukuncin daurin shekara biyar a gidan yarin ga dukkan ma’aikacin da ya yi watsi da dokar.
- Zaben Abuja: Dan jaridar da ke daukar hoton masu sayen kuri’a ya sha da kyar
- Jikan Sardauna, Magajin Garin Sakkwato, ya rasu
Umarnin, wanda Shugaban Kasa, Gotabaya Rajapaksa, ya bayar ranar Asabar, na zuwa ne a daidai lokacin da yajin aikin da ma’aikatan lafiyar kasar ke yi ya shiga kwana na shida, kuma ya tasamma kassara asibitocin gwamnati a kasar.
Sri Lanka dai ta farfado da tsohuwar dokar da ta kafa ne a shekarar 1979, wacce ta haramta wa ma’aikatan bangarorin biyu duk wani yunkurin tsunduma yajin aiki saboda muhimmancinsu ga al’umma.
Dokar za kuma ba kotuna damar yanke hukuncin daurin shekara biyar tare da damar kwace kadarar duk wanda ya karya ta.
Ko a ranar Alhamis din da ta gabata dai sai da ma’aikatan suka yi kunnen uwar shegu da umarnin wata kotu da ta umarce su da su janye yakin aikin har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan karar da aka shigar a kansu.
Sai dai duk da umarnin, kungiyoyin kwadago na ma’aikatan sun ki janye yajin aikin, inda suka ce suna kan tattauna da lauyoyinsu a kan lamarin
Ma’aikatan Sri Lanka dai na neman karin albashi da kudaden alawus-alawus ne, a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki.
Dubban ma’aikatan ne dai suka shiga yajin aikin, lamarin da ya sa bangaren ba da agajin gaggawa na asibitocin gwamnati ne kawai ke aiki a kasar.
A nasu bangaren kuwa, ko da yake ma’aikatan lafiya ba sa cikin yajin aikin, amma sun yi barazanar bin sahun takwarorin nasu matukar gwamnatin kasar ba ta janye yunkurinta na sayar da wutar lantarkinta ga wani kamfanin kasar Amurka ba.