✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara biyan mata masu juna biyu N5,000 duk wata a Jigawa

An bullo da tallafin ne domin su rika zuwa awon ciki da kuma zuwa asibiti yayin haihuwa.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta kammala shiri tsaf domin fara biyan mata masu juna biyu akalla su 5,000 da aka dauki bayanansu alawus din N5,000 a kowane wata.

Mataimakain Gwamanan Jihar, Mallam Umar Namadi, ne ya bayyana hakan yayin wata zantawarsa da manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar.

Ya ce Jihar ta bullo da shirin ne domin ya taimaka wa mazauna yankunan karkara su rika zuwa awon ciki da kuma zuwa asibiti domin haihuwa.

Malam Umar ya kara da cewa tuni gwamnati ta sanya shirin a cikin kasafin kudinta na shekarun 2021 da 2022.

Mataimakain Gwamnan ya ce suna sa rana kudaden za su taimaka wa matan wajen sayen abincin da zai inganta lafiyarsu da ta ’ya’yan cikin nasu saboda kare su daga kamuwa da cutar yunwa.

Ya ce tuni aka bude wa kimanin mata 3,800 asusun ajiya na banki kuma za a fara biyansu a watan Fabrairun 2022, yayin da suke kokarin magance matsalar da ta shafi sauran ragowar mata 1,200.

Malam Umar Namadi ya ce an zabo matan ne daga mazabun siyasa 287 na Jihar domin fara shirin a matsayin gwaji, kafin daga bisani a fadada shi da zarar wannan ya samu nasara.