Kasar Birtaniya ta ce za ta fara ba da takardar izinin shiga kasarta kyauta ga wadanda ke da takardun shaidar digiri na farko da na biyu da na uku domin yin aiki a kasar.
Bangarorin da za a dauki ma’aikatan sun hada da fannin Kimiyya da Fasaha da Kere-kere da kuma sana’o’in hannu.
- Daukar hoto tsirara a gaban ‘bishiya mai tsarki’ ya jawo wa ’yan Rasha kora daga Indonesia
- Dan siyasa ya yi murabus saboda kallon bidiyon batsa a zauren Majalisa
Takardar izinin za ta bai wa wadanda suka same ta damar komawa kasar da zama ko da ba sa aiki.
To sai dai akwai togaciya ga hakan domin ya takaita ne ga daliban da suka kammala karatu a Najeriya ne.
Birtaniya dai na daga cikin kasashe kalilan da yan Najeriya suke son komawa zama cikinta.
Sabon tsarin ba da takardar izinin da zai fara aiki a ranar 30 ga watan Mayu, na bukatar masu sha’awa da su zamto sun kammala karatu daga sanannun jami’o’in Najeriya 50 a kididdigar manyan jami’o’i ta duniya.
Ministan Shige da Fice na Birtaniyan Kevin Foster ya ce kasar ta fito da wannan tsari ne domin zakulo dalibai masu hazaka daga kasashen ketare domin zama a kasar tsawon shekaru 3.
Binciken Aminiya
Kazalika, Gwamnatin Birtaniyan ta ce za ta dings tattara jadawalin jami’o’in duk shekara, kuma za su hada da na manyan jami’u 50 da suka fada rukunin QS da na matsayin jami’o’in a duniya.
Bugu da kari dole mai neman takardar ya zamanto dan Najeriyar na da takardar shaidar digirin farko daidai da na Birtaniya.
To sai dai binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa babu wata jami’a a Najeriya da ke cikin manyan jami’o’i 50 na duniya da rahotan baya-bayan nan da Gwamnatin Birtaniyan ta fitar.
A hannu guda kuma Ministan ya ce sai ya zamo mutum na da akalla Yuro 2,270 a asusun banki na tsawon kwana 28, wata guda kafin neman takardar izinin.
To sai dai ga duk wanda ya fi shekara a can Birtaniyan ba a bukatar sai sun cika wadancan sharuddan.
Haka kuma za iya zuwa da miji ko mata ko dan uwa ga mara aure.
To sai dai ga wadanda ba su da aure sai sun kawo shaidar kasancewa tare na fiye da shekaru biyu, kuma ya zamto alakarsu sahihiya ce.