✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a dawo da ’yan Najeriya sama da 5,000 da ke zaune a Amurka

Wannan dai na zuwa ne tun bayan rantsar da Shugaba Trump, wanda ya yi alƙawarin kame baƙin haure.

Sama da ’yan Najeriya 5,000 da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba, na fuskantar barazanar dawo da su gida.

Daga cikinsu, kusan 1,500 ne ake tsare da su, wanda hakan na daga cikin matakin da sabon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauka na korar baƙin haure da masu neman mafaka ba bisa ƙa’ida ba.

Alƙaluman da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE), ta fitar a watan Nuwamban 2024, sun nuna cewa akwai mutum miliyan 1.445 baƙin haure da ke zaune a ƙasar ba tare da takardun izini ba, ciki har da mutum 3,690 daga Najeriya.

Sai dai sabbin alƙaluman da ICE ta sake fitarwa, sun nuna cewa an ƙara samun wasu mutum 1,454 daga Najeriya da ake tsare da su, kuma ana shirin dawo da su gida.

Hukumar ta ce daga cikin waɗanda ake tsare da su, 772 na jiran hukunci, yayin da aka riga an yanke wa wasu hukunci saboda laifuka daban-daban, ciki har da na karya dokokin shige da fice.

Duk da cewa Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Sai dai hukumar da ke kula da ’yan Najeriya a ƙasashen waje ta ce ta kafa wani kwamiti da zai binciki matsalar tare da duba hanyoyin da za a bi domin magance ta.