Shugaban Hukumar Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC), Birigediya Shu’aibu Ibrahim ya ce duk wanda aka kama da kayan hukumar to za a yanke masa hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari.
Ya bayyana haka ne bayan wasu zauna-gari-banza sun haura sananin NYSC da ke Kubwa a Abuja, da sunan neman kayan tallafi, suka wasashe abubuwa daga dakin ajiyar sansanin.
- Sojoji sun harbi ‘barayin abinci’ a sansanin NYSC na Abuja
- Yadda aka farfasa rumbunan abinci a Abuja
- An ci gaba da fasa rumbunan adana kayan abinci a Abuja
- Yadda ake fargabar karancin man fetur a Abuja
“Ba mu da kayan tallafin COVID-19 a sansaninmu.
“Abun takaici sun sace kayan da ake amfani da su domin ba da horo.
“Doka ce duk wanda aka kama da kayan masu yi wa kasa hidima [ba bisa ka’ida ba] zai fuskanci hukuncin shekara uku a gidan yari”, cewarsa.
Ya kara jan hankalin bata-garin da suka kwashi kayayyaki a sansanin da cewa lallai su dawo da su kafin bincike ya gudana.
Ya ce an kafa hukumar ce domin yi wa kasa hidima da samar da ci gaban kasa, don haka ba su da wata alaka da kayan tallafin annobar COVID-19.