Gwamnatin Nijar ta bayyana shirin daukan sabbin sojoji kimanin dubu biyar a kokarin da ta ke yi na ci gaba da karfafa matakan da za su taimaka a murkushe matsalolin tsaron da suka addabi kasar.
Wannan mataki dai na zuwa ne sanadiyar lalacewar al’amura a yankin sahel da kewayen tafkin Chadi.
- Ramadan: A soma laluben wata ranar Juma’a —Sarkin Musulmi
- Za a hukunta dan sanda saboda sakaci da aiki a Gombe
Haka na kunshe cikin sanarwar da aka bayar ta shafin info militaire mai kula da labaran da suka shafin sha’anin tsaro.
Hukumomin Nijar din sun bayyana shirin soma gudanar da aikin tantance matasan da ke bukatar shiga aikin soja a fadin kasar.
Sabbin matasa akalla dubu biyar ne ake bukatar shigarwa a wannan fanni a yayin aikin tantancewar da za gudanar daga ranar 1 zuwa 31 ga watan mayun 2022 adadin da ya zarta soja 2000 da aka saba dauka a shekarun baya.
Gidan Rediyon Amurka ya ruwaito tsohon Ministan Tsaron kasar, Kalla Moutari yana cewa la’akari da yanayin da ake ciki a yanzu ya kai matsayin da za a kara jan damara.
Matasa ’yan Nijar masu shekaru 18 zuwa 25 da haihuwa ne ake fatan ganin sun shiga wannan aiki, dalili kenan wani jagoran matasa Mohamed Sidi ke kiran takwarorinsa su ba da hadin kai ga wannan yunkurin na kare martabar kasa.
Mai sharhi a kan sha’anin tsaro Alkassoum Abdourahaman na gargadin wadanda aka dora wa alhakin gudanar da wannan aiki su dage akan mutunta ka’idodi domin tabbatar an dauki matasan da suka cancanci shiga aikin soja.
Kara yawan dakarun tsaro da bayar da cikakken horo da samar da nagartattun kayan aiki abubuwa ne da shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya sha alwashin maida hankula a kansu.
Shugaba Bazoum ya yi wannan alkawari ne a yayin da yake gabatar da tsarin jadawalin ayyukan inganta sha’anin tsaron kasa wato Poltique Nationale de la Defense da ya gabatar a watan Oktoban 2021 a makarantar horon manyan hafsoshin soja ta Ecole Militaire Superieure Du Niger da ke birnin Yamai.