✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a dauke ruwan famfo na kwana 5 a Abuja —Hukuma

Za dauke ruwan daga ranar Litinin 18 zuwa Lahadi 24 ga Oktoba, 2021.

Hukumar Kula da Ruwan Sha ta Abuja ta ce za ta toshe wasu hanyoyin ruwa famfo na tsawon kwana biyar domin gudanar da wasu gyare-gyare a matatar ruwa.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce bayan toshe hanyar ruwan, za a hada bututun ruwa na bayan gari da babban bututun ruwa na Kubwa wanda zai yi sanadiyyar dauke ruwan famfo na tsawon kwanaki.

Aikin bututun ruwan da za a gudanar cikin kwana biyar a mako mai zuwa zai gudana ne a ranar Litinin da Talata 18 da 19 sai kuma ranar Juma’a 22 zuwa Lahadi 24 ga watan Oktoba da muke ciki.

Hukumar ta bukaci mazauna yankunan da aikin zai shafa su kasance cikin shiri sannan su tanadai abubuwan da suke bukata na tsaon kwanakin da za a yi aikin.

Unguwannin da abin zai shafa su ne Maitama, Asokoro, Garki 1 Garki 2, sai kuma Wuse 1 da Wuse 2.

Sauran sun hada da Karu, Nyanya, Kubwa 1, Kubwa 2, Barikin Sojoji da kuma Kwaryar Birnin Abuja, wato Central Area.