✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a ci tarar Naira miliyan 1 ga duk wanda ya nuna wa nakasassu wariya

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar hana nuna wa nakasassu wariya a shekaranjiya Laraba. Dokar dai ta haramta nuna wa nakasassu kowane irin…

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar hana nuna wa nakasassu wariya a shekaranjiya Laraba.

Dokar dai ta haramta nuna wa nakasassu kowane irin wariya ko musgunawa, kuma duk wanda ya yi haka, dokar za ta hukunta shi da tarar Naira dubu 100 ko kuma a daure shi a kasso na tsawon wata shida. Ga kamfani ko ma’aikatar gwamnati da suka nuna wariya ga nakasassu kuwa, za a ci su tarar Naira miliyan daya.

Mai taimaka wa Shugaban Kasa ta fuskar Majalisar Dattijai, Sanata Ita Enang ya ce sabuwar dokar za ta ci gaba da gudana har nan da shekara biyar, inda za a kai ga sabawa da ita. Ya ce za a yi wa gine-ginen gwamnati da ababen hawa na gwamnati kwaskwarima domin a samar da wuraren da nakasassu za su iya amfani da su yadda ya dace ba tare da wariya ba, wanda hakan zai hada har da kekunan guragu da makamantansu.

“Kafin a gina kowane irin gida ko ma’aikata ta gwamnati, dole ne a kula da tanadin nakasassu. Duk wata hukuma ko cibiyar gwamnati da ke kula da tsarin gine-gine, ba za ta ba da izini ga duk wani tsarin ginin da ya ki cika tanadin wannan doka ba, wato idan ginin bai samar da tsarin yadda nakasassu za su yi amfani da shi ba,” inji shi.

Ya ce duk wani jami’in gwamnati da ya ba da umarnin yin wani gini na gwamnati, ba tare da an cika sharuddan wannan doka ba, to ya aikata laifi, don haka za a ci shi tarar akalla Naira miliyan daya ko a daure shi na shekara biyu, ko kuma ma a hada masa duka biyun.

“Duk wani nau’in nuna wariya ko wulakantawa, sun haramta a yi wa nakasassu a wuraren shiga mota ko a wani wuri na mu’amalar jama’a, wadanda suka hada da tashoshin jirgin ruwa ko na sama ko na kasa da sauransu. Hakkokin nakasassu sun hada da ilimi, lafiya kuma dole ne a ba su muhimmanci ta fuskar wurin zama ko wajen taimakon farko idan matsala ta faru a wuri. Haka kuma kowace ma’aikata, dole ne ta ware kashi 5 cikin 100 na guraben aikinta ga nakasassu,” inji Sanata Enang.

Ya ce kuma dokar ta tanadi a kafa hukuma ta musamman mai kula da al’amuran nakasassu, wacce za a nada Babban-Sakatare a matsayin shugabanta kuma dole ya kasance daya daga cikin nakasassu.