Bayan tsallake matakin ‘Quarter-Final’ da kasashen Kamaru, Masar, Burkina Faso da Senegal suka yi, za su ci gaba da fafatawa a matakin semi-final.
A ranar Laraba da misalin karfe 8 na dare za a barje gumi tsakanin tawagar ’yan wasan kasar Burkina Faso da Senegal a filin wasa na Ahmadou Ahidjo da ke kasar Kamaru, inda a ke gudanar da Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta 2021.
- Rashin tsaro: ‘Najeriya ce kasa ta 8 mafi hadari a duniya’
- Daga Laraba: Yadda labaran karya ke hana ruwa gudu a cikin al’umma
Kasashen biyu, kowane na da kwararrun ’yan wasa da ke murza leda a kasashen Turai, wanda hakan zai ba wa wasan armashi.
Senegal na da zaratan ’yan wasa irin su Sadio Mane, Idriss Gana Gueye, Kalidou Koulibaly da sauransu, ita kuma kasar Burkina Faso tana da manyan ’yan wasa kamar su Herve Koffi, Traore, Tapsoba da sauransu.
Tawagar ’yan wasan kowanne daga cikin kasashen biyu dai ba tayan baya ba ne.
Kazalika, a ranar Alhamis kuma mai masaukin baki Kamaru ce za ta gwada kwanji da kasar Masar a wasan dab da na karshe a gasar ta AFCON.
Kamaru dai ta shiga gasar da kafar dama, inda tuni ’yan wasanta biyu — Vicente Aboubakar da Toko Ekambi — suke kan gaba wajen zura kwallaye mafi yawa a gasar.
Kamaru na da fitattun ’yan wasa da suka yi fice kamar su Toko Ekambi, Vincent Aboubakar, Zambo Anguida da Andres Onana.
A nata bangaren, Masar na da fitattun ’yan wasa irin su Mohamer Salah, Mohammed Elneny, Mohamer El-Shanawy, Hegazy da sauransu.