Gwamnatin Tarayya ta ce ta fito da wani shiri na ci gaba da aikin ginin manyan hanyoyin tarayya guda 10 da aka fara.
Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, wanda ya bayyana haka ranar Litinin ya ce tsawon hanyoyin ya kai kilomita 2,275 daga cikin kilomita 35,000 na hanyoyin Gwamnatin Tarayya.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga ‘yan Kwamitin Ayyuka na Majalisun Tarayya.
Fashola ya ce ayyukan za su ci gaba da gudana ne karkashin wani shiri mai taken “Ingantawa da kuma Kula da Manyan Hanyoyi” na gwamnatin tarayyar.
A cewar ministan, rukuni na farko na aikin ya kunshi hanyar Benin zuwa Asaba, Abuja zuwa Lokoja, Kaduna zuwa Kano, Anaca zuwa Owerri zuwa Aba, Shagamu zuwa Benin, Abuja zuwa Keffi zuwa Akwanga, Kano zuwa Maiduguri, Lokoja zuwa Benin, Enugu zuwa Fatakwal, da kuma Ilori zuwa Jebba.
- Jam’iyyar PDP ta yi amfani da hotonan hanyoyin Laberiya don bata Fashola
- Za a daina biyan jihohi kudaden gyaran titunan tarayya
- Hana bara a kan tituna a jihohi uku
“Mun shigo da kamfanoni masu zaman kansu ne saboda mu takaita yawan tsaikon da ake samu yayin aiwatar da ayyukan sakamakon karancin kudade a baya”, inji Fashola.
Ya ce shirin zai samar da kudaden aiwatar da manyan ayyuka da kudinsu ya kai Naira biliyan 163 da miliyan 23 tare da samar da ayyukan yi sama da 23,000 ga ‘yan kasa. Sannan gina manyan hanyoyin zai rage yawan hadurran da ake samu a kansu.
Da suke mayar da martani, ‘yan majalisar sun jinjina wa gwamnatin saboda wannan hobbasa da ta yi, ko da yake sun nuna shakku kan ko ‘yan kwangilar za su iya aiwatar da ayyukan.