A ranar Juma’a 4 ga watan Fabrairu ne za a bude gasar wasannin Olympics na hunturu na shekarar 2022 a Beijing, babban birnin kasar China.
Wasannin Olympics na bana da a hukumance aka yi wa lakabi da XXIV Olympic Winter Games, zai gudana ne kai tsaye daga ranar 4 zuwa 20 ga watan Fabrairun 2022.
- Mata sun ci gaba da karatun jami’a a Afghanistan
- Kisan Hanifa: An mayar da shari’ar gaban Babbar Kotu
Za a gudanar da wasannin ne a Beijing da kuma wasu garuruwa da ke makwabtaka irinsu Yanqing da Chongli duk a kasar ta China.
Sai dai a yau Laraba, 2 ga watan Fabrairu, an fara gasar da wasu wasanni na sharar fage a tsakanin tawagar wasu kasashe da suka hada da Sweden da Birtaniya, Australia da Amurka, Norway da Jamhuriyyar Czech sai kuma China da Switzerland.
Tun a watan Yulin 2015 aka zabi Beijing a matsayin birnin da zai yi wa wasannin masaukin baki yayin Babban Taron Kwamitin Wasannin Olymopics karo na 128 da aka gudanar a Kuala Lumpur, babban birnin kasar Malaysia.
Wasannin Olympics na hunturu na 2022 shi ne irinsa na farko da za a gudanar a China, kuma shi ne cikon na uku a jere da za a gudanar a yankin Gabashin Nahiyyar Asia.
Na bayannan sune wadanda suka gudana a birnin Pyeongchang na Koriya ta Kudu a shekarar 2018, sai kuma wanda aka gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan a shekarar 2020.
Haka kuma, China ta kasance kasa ta farko a duk fadin duniya da ta karbi bakwancin wasannin Olympics iri biyu na hunturu da kuma na lokacin kaka.
Akwai wasu wurare da aka gina tun a lokacin wasannin Olympics na kaka a shekarar 2008 da a yanzu za a ribace su a bana, inda kuma za a yi amfani da filin wasanni na Beijing a matsayin farfajiyar da za a gudanar bikin budewa da kuma rufe wasannin.
Sai dai tun watannin baya bayan nan aka rika bayyana fargaba a kan kalubalen da sabon nau’in Coronavirus na Omicron da ka iya zama barazana ga wasannin Olympics da ke tafe.
Da wannan ne mahukunta a Beijing suka yi gargadin cewar sabon nau’in Coronavirus na Omicron da ke saurin yaduwa a cikin al’umma zai janyo kalubale a wasannin Olympics musamman la’akari da lokacin sanyin hunturu da zai gudana.
A wani jawabi a game da bullar sabon nau’in na coronavirus da ya yi tun a watan Nuwambar bara, mai magana da yawun Ma’aikatar Wajen China, Zhao Lijian ya bayyana cewar za a fuskanci kalubale, amma kasancewar kasar ta sha fama da wannan cutar wacce suka yi nasarar dakile ta, za su yi duk mai yiwuwa na ganin wassannin ya kankama ba tare da fargabar baza cutar ba.
Kamar dai yadda ta kasance a wasannin Olympics na kaka da aka gudanar a watanni shida da suka gabata a Tokyo, haka shi ma wannan an yi tanadin matakan kariya da dakile yaduwar cutar Coronavirus kamar yadda mahukuntan lafiya suka shar’anta.
Haka kuma sauran ababen fargabar da aka rika jingina wa wasannin Olympics na bana sun hada da yanke alakar diflomasiyya da China bisa zarginta da ake yi da kisan kare dangi da take yi wa ’yan kabilar Uyghur musulmi ganin yadda hukumomin kasar ke azabtar da su ta hanyoyin da Majalisar Dinkin Duniya ta haramta.
Wannan ya sanya a halin yanzu kasashe da dama suka rika tura ’yan wasan da za su yi masu wakilci ba tare da wani Minista da wakili a gwamnatace ba.
Dubban ’yan wasa da ’yan jarida gami da wadanda za su halarci wasan daga wasu kasashen duniya tuni an kebe su har na wani lokaci kafin gudanar da wasannin.