Makarantun sakandare a Najeriya za su ci gaba da karatu daga ranar 4 ga Agusta 2020, nan take bayan dawowa daga hutun Babbar Sallah.
Gwamnatin Tarayya ta ce za a bude makarantun ne ga dalibai masu rubuta jarabawar kammala makarantun sakandare kadai.
“Mun amince cewa azuzuwan JS3 da SS3 za su koma makaranta da zarar hutun Sallah ya kare domin su sami damar shiryawa kafin fara jarabawar WAEC a ranar 17 ga watan Agustan 2020.
“Tattaunawar ma’aikatar da kungiyar malamai ta kasa (NUT) da masu makarantun kudi da kwamishinonin ilimi da ma hukumomin jarabawa a fadin Najeriya ta amince da a bude makarantun nan take”, inji Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Ben Bem Goong ya fitar a ranar Litinin, ta ce taron ya cimma matsayar yin kira ga Gwamnatin Tarayya ta hanyar kwamitin kar-ta-kwana don yaki da annobar COVID-19 da ma sauran masu hannu da shuni a kasar da su tallafa wa makarantu wajen shirye-shiryen budewar.
Sanarwar ta kuma ce a ranar Talata ma’aikatar ilimin da kuma shuwagabannin hukumomin da su ke shirya jarrabawar na NECO, WAEC, NABTEB da NBAIS za su tattauna domin daidaita jadawalin jarabawar nasu wanda ma’aikatar za ta fitar daga bisani.
Makarantu dai a Najeriya sun kasance a rufe tun a watan Maris bayan gwamnati ta bayar da umarnin yin haka saboda fargabar annobar ta COVID-19.