Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta gudanar gagarumin bincike don gano musabbabin samun gurbataccen man fetur a kasar.
Karamin Ministan Fetur Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a ranan Laraba yayin ganawarsa da manema labarai bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Kasa a Fadar Gwamnatin Najeriya.
- AFCON 2021: An yi wa tawagar Senegal ruwan kudi da filaye
- Matsalar kashe-kashe don yin tsafi ta fusata Majalisar Wakilai
Duk da cewa ministan bai bayyana kamfanonin da lamarin zai shafa ba, sai dai ya ce za a bayyana sunayensu idan an kammala binciken.
“Za a yi gagarumin bincike don fayyace komai. Akwai bukatar mu gano komai da komai kafin mu dawo mu sanar da ku abin da zai faru da miyagun,” a cewar ministan.
’Yan Najeriya da dama na kokawa kan gurbataccen man fetur da suka sha a gidajen mai na kasar da kuma dogayen layi da ake yi kafin samun sa.
Sai dai shugaban sashen dakon man na kamfanin NNPC ya bayyana dalilin da ya sa ake samun layukan da kuma matakin da aka dauka.
Tun a ranar Talata da ta gabata ce Shugaban kula da dokokin ma’aikatar man fetur ta Najeriya, Malam Faruk Ahmed, ya yi cikakken bayani a game da akasin da aka samu a game da gurbataccen man fetur a wasu sassan kasar.
Shugaban ya yi bayani ne a kan yadda gurbataccen man ya shiga wasu gidajen mai a kasar wanda ya sanya al’umma cikin fargaba da karanci a samun man fetur don gudanar da ayyukansu na sufuri na yau da kullum.
A wata hira ta musamman da shugaban na ma’aikatar dokokin man fetur, Faruk Ahmed, ya bayyana akasin da aka samu a matsayin ya zo ba a zata sakamakon yadda aka kwashe sama da shekaru 30 ba a fuskanci irin wannan yanayi ba.
Ma’aikatar dokokin man fetur din dai ta ce zata dauki matakan da suka dace a kan kamfanin da aka yi yarjejeniyar shigowa da man fetur din cikin Najeriya da shi sakamakon yadda ta gano kamfanin da ya aikata hakan bayan bincike mai zurfi.
Kamfanin da aka gano ya shigo da gurbataccen man wanda ke da sinadarin Mathanol da ya wuce kima dai ya shigo da jiragen ruwa na man da ya kunshi tan dubu 30 ne kan tekun kasar wanda da zarar aka gano, ma’aikatar dokokin man fetur din ta maida jirage 3 cikin hudu kasar da ta shigo wa Najeriya da su.
Shi ma kamfanin NNPC zai dauki matakan da ya dace kan wannan batu kamar yadda Malam Faruk Ahmed ya bayyana.