Majalisar Dattawa ta yanke shawarar gudanar da bincike a kan yadda tsohuwar Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi amfani da basukan naira tiriliyan 30 da ta karɓo daga Babban Bankin Najeriya CBN.
Ana iya tuna cewa dai Gwamnatin Buhari ta yi amfani da wani tsari da CBN ya kira ‘Ways and Means’ da ya riƙa samar mata da kuɗaɗen toshe gibin da aka samu a kasasfin kudinta.
Sai dai Majalisar Dattawan ta ce yadda aka kashe wadannan kuɗaɗen da aka karɓo daga CBN a karkashin jagorancin Godwin Emefiele ba bisa ka’ida ba ne kuma matsalar abinci da kasar ke fuskanta a yanzu shi ne sila.
Dangane da hakan ne Majalisar Dattawan ta yanke shawarar kafa wani kwamitin da zai gudanar da bincike a kan yadda gwamnatin Buhari ta kashe kuɗaɗen, tana mai nuni da cewa da gangan aka ki bai wa majalisar dokokin kasar bayani a kan yadda aka kashe kuɗaɗen.
Kwamitin, wanda a Larabar nan za a ƙaddamar da shi, zai kuma binciki yadda aka ba da bashin naira biliyan 10 a karkashin shirin rancen manoma na Anchor Borrowers, da kuma hada-hadar kuɗaɗen musanya na kasashen waje da ya kai dala biliyan 2 da miliyan dari 4.
Majalisar ta kuma soki jagoranci tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, dangane da yadda ya yi wa akalar jagoranci riƙon sakainar kashi har aka karɓo wannan bashin mai tarin yawa.
Sai dai da yake martani yayin zaman majalisar na ranar Talata, Sanata Lawan ya ce adadin bashin kuɗaɗen na tsarin ‘Ways and Means’ da majalisar ta sahale wa tsohuwar Gwamnatin Buhari naira tiriliyan 23 ne sabanin naira tiriliyan 30 da ake takkadama a kai a yanzu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsadar abinci da hauhawar farashin kayayyakin masarufi, faɗuwar darajar naira da matsalar tsaro ke ci gaba da ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya.
Shugaba Bola Tinubu na ci gaba da shan caccaka tun bayan janye tallafin man fetur da ya yi, tare da mayar da tsarin canjin kuɗaɗen musayar bai ɗaya suka jefa al’ummar kasar cikin matsanancin kuncin rayuwa.