Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun daraktanta na watsa labarai da hulda da jama’a, Misis Adenike Adeyemi, ya bayyana ce wa, shugaban hukumar, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim.
- FCE Gombe za ta koma karatu ranar 9 ga Nuwamba
- ASUU ta gindaya wa Gwamnati sharadin janye yajin aiki
- KAROTA za ta dauki karin ma’aikata
Ya ce, hukumar (NYSC) ba ta taba samun rahoton wani daga cikin masu hidimar kasa ya kamu da cutar ba, tun farkon samun rahotan bullar cutur a kasar nan.
Sanarwar ta kara da cewa shugaban ya bayyana hakan yayin wani kwarya-kwaryar taron wayar da kai da aka shirya wa matasa masu hidima ‘yan rukunin ‘B’ a kan cutar da ya gudana a birnin Jos na jihar Filato.
Shugaban ya ce hukumar za ta ci gaba da wayar da kan matasan har sai an fita daga yanayin mayuwacin halin da ake ciki, don samun nasarar gudanar da hidimar kasar cikin nasara.
Shu’aibu ya ce hukumar ta himmatu wajen tabbatar da ba’a samu ko mutum daya daga sansanin masu hidimar kasar ya kamu da annobar Covid-19 ba.
Ya ce, annobar corona sai da ta tilasta rufe rukunin masu hidimar kasa rukuni na daya na 2020 saboda gudun yaduwar annobar a sansanonin masu hidimar kasar.
Hukumar ta ce ta tanadi dukkan kayan kare yaduwar cutar ga masu hidimar kasar a yayin bude sansanin mai zuwa a dukkan fadin kasar nan.