Majalisar Wakilai na bincike kan Naira biliyan 186 da aka yi ikirarin kashewa a shirin ciyar da dalibai na Gwamnatin Tarayya daga shekarar 2016.
Majalisar ta bukaci bayanan ne a lokacin da babbar jami’ar shirin Sinkaye Temitope ta gurfana a gaban kwamitin bin diddigin kudade na majalisar a ranar Litinin.
Da take jawabi, jami’ar ta ce shirin, wanda aka fara tun shekara ta 2016 kafin kafa Hukumar Jin-kai da Kai Agajin Gaggawa kuma a lokacin yake karkashin shirin tallafa wa marasa karfi na gwamnatin ya lakume kudi har Naira biliyan 186.
A cewarta, Naira biliyan 62 da miliyan 200 aka kashe a 2018, sai biliyan 32 da miliyan 200 a 2019, yayin da Naira biliyan 124 da miliyan 400 kuma aka kashe a shakarar da muke ciki ta 2020.
- NCDC ta kora dalibai gida a Kuros Riba
- Majalisar Dattawa ta yi barazanar ba da umarnin kama Lai Mohammed
To sai dai yayin da yake mayar da martani, shugaban kwamitin bin diddigin, Oluwole Oke ya ce sam ‘yan majilisar ba su gamsu da yadda aka kashe kudaden ba.
Kwamitin ya kuma bukaci a yi masa cikakken bayanin yadda aka kashe wasu Naira biliyan 64 daga cikin kudaden da aka kashe na ciyar da daliban.
‘Yan majalisar sun kuma nuna rashin gamsuwarsu kan wata takarda da ta nuna cewa kwamitin ya ciyo bashin Dala miliyan 400 daga Bankin Duniya, Dala miliyan 321 daga kudaden Abacha da aka kwato sai kuma Dala miliyan 400 da aka karba daga asusun gwamnati.
Kwamitin ya ce za su bi takardun daki-daki don tabbatar da ko an bi ka’ida yayin kashe kudaden.