✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4

Ƙudirorin sun tsallake karatu na biyu a yayin zaman majalisar da ya gudana a ranar Laraba.

Majalisar Wakilai ta ɗauki mataki na gaba wajen ƙirƙirar sabbin jihohi huɗu a Najeriya.

’Yan majalisa sun tattauna tare da amincewa da karatu na biyu na ƙudirorin da ke neman kafa jihohin Oke-Ogun, Ijebu, Ife-Ijesa, Tiga, Orlu, da Etiti.

Waɗannan ƙudirori na daga cikin yunƙurin sauya kundin tsarin mulkin 1999.

Shugaban masu rinjaye na majalisa, Hon. Julius Ihonvbere, wanda ya gabatar da ƙudirorin, ya jaddada muhimmancinsu.

“Waɗannan ƙudirori suna nuna buƙatun yankuna daban-daban na ƙasa domin samar da ingantaccen shugabanci da rarraba albarkatu cikin adalci,” in ji shi.

Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman, ya jagoranci kaɗa ƙuri’ar murya inda ƙudirorin suka samu amincewa.

An tura su zuwa kwamitin majalisa kan sauya kundin tsarin mulki domin ci gaba da nazari.

Ɗaya daga cikin masu ɗaukar nauyin ƙudirin, Hon. Ghali Mustapha Tijani, ya ce, “Kafa Jihar Tiga zai kusanto da gwamnati ga jama’a tare da haɓaka ci gaba.”

Ana buƙatar amincewar majalisun dokokin jihohi da na ƙasa kafin ƙirƙirar sabbin jihohin a Najeriya.