Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu.
Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar.
- Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya
- Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya
Ƙudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar.
Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin bayan cece-kucen da hakan ya haifar a faɗin ƙasar.
Ƙudurorin na daga cikin gwamman ƙudurorin da majalisar ke nazari a kansu, a wani ɓangare na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.
Aminiya ta ruwaito cewa, majalisar ta janye ƙudirin ne bayan gwamnatocin jihohin sun bayyana adawarsu kan matakin da ke neman tuɓe musu rigar alfarmar da ke bai wa gwamnoni da mataimakansu da kuma mataimakin shugaban ƙasa kariya daga fuskantar tuhuma kan laifuka.
A ranar Larabar da ta gabata ce ƙudirin ya samu karatu na biyu a zauren majalisar, ƙarkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu.