✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaɓen cike gurbi: ’Yan sandan Kano sun gargadi magoya bayan APC da NNPP

A shirye muke mu tunkari duk wani ko wata kungiyar da ta yi yunkurin haddasa rikici a lokacin zaben.

Gabanin sake gudanar da zaben dan Majalisar Dokoki mai wakiltar mazabar Kunchi (Gari) da Tsanyawa da za ake shirin gudanarwa a watan gobe, Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ja kunne manyan jam’iyyun siyasa da kada su kuskura su kawo tarzoma ko kuma tada zaune tsaye a jihar.

Kwamishinan ’Yan sandan jihar, Muhammad Usain Gumel ne ya yi wannan gargadin.

CP Gumel ya ja kunne shugabannin jam’iyyu da su gargadi magoya bayansu kan yin duk wani abu da ka iya kawo cikas wajen gudanar da zaben.

Manyan jam’iyyun siyasa biyu da za su fafata a zabe su ne, APC da NNPP, inda dukkan su, suka kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da yin alkawarin bin ka’idoji a lokacin zabe da kuma bayansa.

Gumel ya yi wannan gargadin ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasa, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki.

“A yau, mun zo ne domin tattaunawa a tsakaninmu kan hanya mafi dacewa da za a sake gudanar da zaben cikin lumana,” inji shi.

Kwamishinan ‘yan sanda Gumel ya kuma gargadi ‘yan siyasa da magoya bayansu da su kauce wa daukar duk wani mataki da zai haifar da rikici a lokacin zaben.

Ya bayyana cewa, “Hukumomin tsaro na ‘yan sanda da ‘yan uwa a shirye suke su tunkari duk wani ko wata kungiyar da ta yi yunkurin haddasa rikici a lokacin zaben.

Shi ma da yake jawabi, Kwamishinan Hukumar Zabe na Kano, Ambasada Zango ya ce, hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zaben.

Ya kara da cewa, an kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaben ba tare da tangarda ba, inda ya kara da cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a matsayinta na jigo za ta yi wa duk bangarorin da abin ya shafa daidai kamar yadda dokar zabe ta tanada.