Rasuwar Alhaji Yusuf Maitama Sule Xanmasanin Kano a ranar Litinin 3 ga Yulin bana yana da shekara 88, ta raba Najeriya da xaya daga cikin fitattun dattawanta masu faxa-a-ji, kuma ana iya cewa na qarshe a cikin fitattun gwanayen iya magana da suka faro daga Jamhuriyya ta Farko.
Ya rasu ne a wani asibiti da ke qasar Masar bayan ya haxu da matsalar wata cuta a zuciya wadda ta tilasta xauke shi daga asibitin Abdullahi Wase da ke Kano. Jana’izrsa a Kano washegari ta samu halartar dubban mutane da gwamnonin jihohi da dama da manyan sarakuna da kuma wakilan Gwamnatin Tarayya a qarqashin Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Qasa.
Yusuf Maitama Sule wanda aka haife shi a ranar 1 ga Oktoban, 1929, ya halarci makarantar elemantare da ta Midil da ke Kano, kafin ya wuce zuwa Kwalejin Kaduna wadda daga baya ta koma Kwalejin Barewa a 1943.
A 1946 ya halarci wani kwas na horar da malamai inda daga nan ya koyar a Makarantar Midil ta Kano har zuwa 1953. Daga baya an yi masa sauyin wurin aiki zuwa Ma’aikatar Watsa Labarai, saboda qwarewarsa wajen iya magana, inda nan da na ya zama Babban Jami’in Watsa Labarai. Marigayi Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi I ne ya naxa Xanmasanin Kano na farko a shekarun 1950. An zavi Maitama Sule a matsayin xan Majalisar Wakilai a 1959 a qarqashin Jam’iyyar NPC. Kuma daga baya Fira Minista Sa Abubakar Tafawa Valewa ya naxa shi Ministan Ma’adinai da Wutar Lantarki yana xan shekara 29. Shi ne Minista mafi qarancin shekaru a Jamhuriyya ta Farko.
Bayan juyin mulkin 1966 da ya kawar da Jamhuriyya ta Farko, sai ya koma Kano ya kama aiki da Majalisar Masarautar Kano. Kuma lokacin da aka qirqiro Jihar Kano a 1967, sai aka naxa shi Kwamishinan Qananan Hukumomi a qarqashin Gwamnan Soja Kwamshinan ’Yan sanda Audu Baqo.
Janar Murtala Muhammad ya naxa shi Kwamshinan Hukumar Sauraren Koke-Koken Jama’a a 1976. Kuma a matsayinsa na mai yanke hukunci na qasa, Maitama Sule ya zagaya qasar nan gaba xaya kuma ya sauke nauyin da aka xora masa yadda ya kamata kafin ya yi murabus bayan dawo da harkokin siyasar jam’iyyu a 1978 inda ya shiga Jam’iyyar NPN.
Ya fafata takara a zaven fid-da-gwani na Jam’iyyar NPN inda ya zo na biyu a bayan Alhaji Shehu Shagari. Kuma a daidai lokacin da ake shirin fafata zagaye na biyu ne, Maitama Sule da Malam Adamu Ciroma suka janye suka bar wa Shagari. A 1979, Shugaban Qasa Shehu Shagari ya naxa shi Jakadan Najeriya a Majalisar Xinkin Duniya da ke birnin New York. A can ya shugabanci Kwamitin Musamman na Majalisar Xinkin Duniya kan Yaqi da Nuna Bambancin Launin Fata, inda ya tafiyar da ayyukansa biyu cikin sadaukar da kai da bayanai masu gamsarwa.
Ya yi ritaya daga harkokin siyasa bayan rushe Jamhuriyya ta Biyu a 1983. Kuma tun daga lokacin Maitama Sule ya tsaya a matsayin wani dattijo da ake neman shawararsa a kowane lokaci, saboda sauqin samunsa da tawali’unsa da ximbin iliminsa game da harkokin siyasar Najeriya ganin yadda ya kasance a sahun gaba a Jamhuriyya ta Farko da Jamhuriya ta Biyu, da qwarewarsa wajen iya magana da sarrafa harshe da kuma cikakkiyar sadaukar da kansa ga kasancewar Najeriya a matsayin dunqulalliyar qasa.
A shekara 30 da suka gabata, Alhaji Yusuf Maitama Sule ya riqa bayyana a matsayin babban baqo mai jawabi a xaruruwa ko dubban tarurrukan lacca da qaddamarwa da gabatarwa da buxe wasu ayyuka. Kullum saqonsa xaya ne: Haxin kan Najeriya da burin zamantakewar a tsakanin mabambantan al’umma da addinai domin mayar da Najeriya wata babbar qasa a nan gaba.
Ya kasance mutum mai kyautata wa iyalinsa. Babban xansa Mukhtar Maitama Sule ya ce, “Mahaifina babban mutum ne kuma uba ga kowa. Ba zan iya qididdige yawan mutanen da ya raina suka taso a qarqashin kulawarsa a wannan gida ba. Waxansu har yanzu suna nan a raye. Kuma dukiyarsa ta kowa da kowa ne.”
Shi kuwa jikansa Alhaji Hassan Mahmoud ya ce shi ne “komai gare mu, mahaifi, mai raino, mai shiryarwa kuma babbansu ginshiqin iyalan.”
A saqon ta’aziyyarsa Shugaban Qasa Buhari ya ce: “Za mu daxe ba mu ga irinsa ba.”
Maitama Sule ya rasu ne a daidai lokacin da rikicin qabilanci ke hauhawa a Najeriya kuma ake buqatar qwarewa da muryarsa domin kwantar da qurar. Ya rasu ya bar ’ya’ya 10 da jikoki da dama. Allah Ya saka wa mutum mai son zaman lafiya Alhaji Yusuf Maitama Sule da gidan Aljanna.