✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunwa ta sa daliban sakandare zanga-zanga a Gombe

Gwamnatin Jihar na bincike kan rashin ba daliban makarantar kwana isasshen abinci.

Daliban makrantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS) ta Jihar Gombe, sun yi zanga-zangar lumana zuwa hedikwatar Ma’aikatar Ilimin Jihar kan abin da suka kira ‘rashin isasshen abinci’ da ake ba su.

An nuno daliban a wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta suna kukan yunwa inda suke cewa sam abincin da ake ba su ba ya isan su.

“An gaya mana cewa hukumar makarantar ce ta sa masu gadi su rika kwace mana abinci,’’ kamar yadda wani dalibi ya bayyana.

Wadansu daliban sun shaida wa Aminiya cewa sun fito zanga-zangar ce saboda abincin da gwamnatin ke ba su baya isar su, kayan abincin da suke kawowa daga gida kuma masu gadin makarantar ke kwacewa.

Koda yake sun ce ana ba su abinci amma kadan ne, shi din ma ana bi ana karbe na wadansunsu, abin da suka ce bai dace ba.

A cewarsu, kwace musu kayan abinci da ma ba su abin da ba ya kosar da su ne abin da ya tunzura su yin zanga-zangar domin gwamnatin ta ji kukansu.

Gwamnati na zargin makarkashiya

Da alama zanga-zangar daliban ta ranar Litinin ta tayar da hankalin gwamnatin jihar inda Kwamishinan Ilimi, Dauda Maji Batari, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa ba yunwa ce ta sanya daliban zanga-zanga ba.

A cewarsa, wani kullanlan shiri ne na yi wa gwamnatin jihar makarkashiya.

Ya ce zanga-zangar ba ta dace ba saboda idan daliabn na da wata matsala akwai hanyar da ta dace su bi wajen bayyanawa; amma kwatsam sai aka gan su suna zanga-zanga har zuwa Ma’aikatar Ilimi.

Kwamishinan ya ce duk korafin da suke da shi kamata ya yi su sanar wa hukumar makarantarsu, kuma za ta saurari kokensu.

Ya musanta cewa akwai karancin abinci a makarantun kwana na jihar domin hukumar da ke da samar da abinci ga makarantun kwanan ta riga samar da abinci tun a ranar 5 ga watan nan na Yuli.

Ya ce tuni gwamnati ta kafa kwamitin mutum bakwai domin gano musabbabin zanga-zangar daliban kuma za a gurfanar da duk mai hannu a ciki a gaban kotu.

An umarci kwamitin da ya mika rahotonsa kafin a tashi a aiki ranar Laraba, 9 ga watan Yuni.