Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yunwa tana ci gaba da ta’adi sakamakon farin da ake fuskanta a kasar Somaliya.
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce farin da ake fuskanta a Somaliya ya kasance mafi muni ga kasar cikin shekaru 50 da suka gabata.
- Shehu Danfodiyo ba ta’addanci ya yi ba —Sarkin Musulmi
- ASUU: An ki bude azuzuwan dalibai a jami’o’in Kano
A wannan Talata mai magana da yawun asusun, James Elder ya ce ana bukatar kimanin kudi Dalar Amurka miliyan dubu biyu saboda a tunkari matsalar.
Jami’in asusun na UNICEF ya kara da cewa a watan Agustan da ya gabata kadai kimanin yara 44,000 aka kwantar a asibiti sakamakon matsananciyar yunwa.
Kimanin mutane miliyan takwas, kusan rabin mutanen kasar ta Somaliya farin ya shafa a cewar Majalisar Dinkin Duniya, dama kasar tana cikin tashe-tashen hankula na tsageru masu kaifin kishin addinin Islama.