✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD

Cutar HIV za ta zama annoba a faɗin duniya sakamakon janye tallafin da Amurka ta yi.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a samu mutum 2,000 sabbin kamuwa da cutar SIDA duk rana a faɗin duniya.

MDD ta ce tana wannan gargaɗi ne sakamakon matakin Amurka na katse taimakon agajin ƙasashen duniya ƙarƙashin Hukumar ta USAID.

MDD ta ce ce tilas ne a maye gurbin taimakon idan ana neman kare duniya daga shiga annobar cutar ta AIDS..

Hukumar ta ce muddun Amurka ba ta dawo da tallafin daƙile cutar ba, kuma ba a samu maye gurbin taimakon na Amurka ba, nan da shekaru huɗu za a samu kimanin mutane miliyan 6.3 sabbin masu kamuwa da cutar ta AIDS ko SIDA, gami da samun ƙarin masu mutuwa daga cutar.

Da take jawabi a Geneva a ranar Litinin, Winnie Byinyama, ta ce za a samu sabbin masu kamuwa da cutar aƙalla guda 2,000 kullum saboda janye tallafin, tana mai cewa tuni dubban likitoci da sauran ma’aikatan jinya sun fara rasa aikinsu.

Sai dai duk da haka ta yaba da gudunmawar Amurka wajen tallafa wa ayyukan kiwon lafiya a duniya a gomman shekaru da suka gabata.

Amma ta ce yadda kwatsam aka dakatar da tallafin ba tare da shiri ba, ya fara kawo tsaiko a ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da cutar ta HIV.

Alƙaluman da aka fitar a shekarar 2023 sun nuna cewa kimanin mutum 600,000 suka rasa rayukansu a faɗin duniya sakamakon Cutar ta SIDA.