Majalisar Wakilai ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki zargin da ake yi wa Hukumar Bayar da Agaji ta Ƙasa da Ƙasa ta Amurka (USAID), da tallafa wa Boko Haram.
An yanke wannan hukunci ne bayan ɗan majalisa, Inuwa Garba, ya gabatar da buƙatar gaggawa a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Garba, ya nuna damuwa game da kalaman da ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi kwanan nan, inda ya zargi USAID da bai wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda, ciki har da Boko Haram tallafi.
Ya jaddada cewa Boko Haram ta haddasa babbar matsalar tsaro a Najeriya sama da shekara 10.
“Scott Perry ya yi wannan iƙirari a wani zaman majalisar dokokin Amurka, inda ya ce ana kashe sama da dala miliyan 697 duk shekara, kuma kai-tsaye ga ƙungiyoyi irin su ISIS, Al-Qaeda, da Boko Haram ne suke amfana,” in ji Garba.
“Boko Haram na da babbar maɓoya a Arewacin Najeriya, don haka akwai yiyuwar sun amfana da wannan tallafi.
“Idan zargin ya kasance gaskiya, hakan babbar barazana ce ga tsaron ƙasa da na duniya baki ɗaya,” in ji shi.
Bayan tattaunawa tsakanin ’yan majalisar, Kakakin Majalisar ya kafa kwamitin bincike na musamman don yin duba a kan lamarin.
Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu masu zuwa.